APPLICATION MAI MATUKAR AMFANI

 APPLICATION MAI MATUKAR AMFANI.

Assalamu alaikum barkanmu da yau  barka da kasancewa da ABDUL TECH HAUSA  Allah ya karɓa mana ibadunmu Ameen.

A rubutun namu na yau zanyi bayani ne dangane da wani app mai suna (App Share) 

App share application ne mai matuqar amfani da zai baka damar tura application a duk inda kakeso.

A cikin wannan app din zaka iya tura App fiye da 100 lokaci daya a duk inda kakeso.

Zaka iya turo Application a Whatsapp Bluetooth Email da xender e.t.c duk a cikin wannan App din.

Bugu da kari har application da bazaka iya sharing nasu a xender ba wannan app din zai baka damar turawa cikin sauki.

Wannan Application zai baka damar tura Uninstall, backup da manage apps.

A cikin wannan app din zakaga dukkanin apps da suke kan wayarka da kuma ya yanayin nauyin apps din yake, a ciki zaka iya uninstall duk app din da kakeso a wayarka.

Idan ka duba zakaga sama da mutane MILLION 10 ne suke amfani da wannan app din suna suna bada kyakkyawar shaida akansa.

Kai ma zaka iya saukewa a wayarka ta hanyar danna wannan link din



https://play.google.com/store/apps/details?id=com.luckydeveloper.apkshare

Allah yasa mu dace🙏

Comments

Popular Posts