APPLICATION MAI MATUKAR AMFANI
APPLICATION MAI MATUKAR AMFANI. Assalamu alaikum barkanmu da yau barka da kasancewa da ABDUL TECH HAUSA Allah ya karɓa mana ibadunmu Ameen. A rubutun namu na yau zanyi bayani ne dangane da wani app mai suna (App Share) App share application ne mai matuqar amfani da zai baka damar tura application a duk inda kakeso. A cikin wannan app din zaka iya tura App fiye da 100 lokaci daya a duk inda kakeso. Zaka iya turo Application a Whatsapp Bluetooth Email da xender e.t.c duk a cikin wannan App din. Bugu da kari har application da bazaka iya sharing nasu a xender ba wannan app din zai baka damar turawa cikin sauki. Wannan Application zai baka damar tura Uninstall, backup da manage apps. A cikin wannan app din zakaga dukkanin apps da suke kan wayarka da kuma ya yanayin nauyin apps din yake, a ciki zaka iya uninstall duk app din da kakeso a wayarka. Idan ka duba zakaga sama da mutane MILLION 10 ne suke amfani da wannan app din suna suna bada kyakkyawar shaida akansa. Kai ...



